Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada ya barke tsakanin sojoji masu goyon bayan shugaba Laurent Gbagbo a kasar Ivory Coast da dakaru masu goyon bayan Alassane Ouattara


Sojojin dake goyon bayan shugaba president Laurent Gbagbo suna kokarin tarwatsa magoya bayan Alassane Ouattara a yankin Aboboa dake birnin Abidjan, 16 Dec 2010

Fada ya barke a tsakanin sojoji masu goyon bayan shugaba Laurent Gbagbo dake kan gadon mulki a kasar IC ko CI da dakaru masu goyon bayan Alassane Ouattara.

Fada ya barke a tsakanin sojoji masu goyon bayan shugaba Laurent Gbagbo dake kan gadon mulki a kasar IVory Coast da dakaru masu goyon bayan Alassane Ouattara. ‘Yan jarida sun fadawa Muryar Amurka cewa, sassan biyu sun yi musanyar wuta da manyan bindigogi da na igwa yau alhamis a kusa da hotel din Golf dake Abidjan, inda Ouattara ya mayar hedkwatarsa. Suka ce an goce da fada a lokacin da masu zanga-zanga dake goyon bayan Ouattara suka yi kokarin fita domin yin maci zuwa gidan telebijin na kasar. Ouattara yayi kira ga magoya bayansa da su yi maci zuwa gidan telebijin na kasar da kuma gine-ginen gwamnatin dake hannun shugaba Laurent Gbagbo. Tun fari a yau alhamisar, ‘yan sanda a birni mafi girma na kasar, Abidjan, sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa magoya bayan Ouattara wadanda suka yi kokarin taruwa. ‘Yan sanda da sojoji sun kakkafa shingaye a kewayen gidan telebijin na kasar a yayin da suke kokarin hana yin maci zuwa wurin. ‘Yan jarida sun ce an kashe mutane akalla uku a wannan tashin hankali. Ouattara da Gbagbo duk su na ikirarin lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka yi a watan da ya shige, kuma kowannensu ya kafa gwamnatinsa, abinda ya haddasa fargabar barkewar sabuwar fitina shekaru 8 bayan yakin basasar da aka yi a kasar. Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Hadin kan Afrika da Kungiyar Tarayyar Turai duk sun amince da Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben, yayin da sojojin kasar kuma suke goyon bayan Gbagbo.

XS
SM
MD
LG