Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Gwamnatoci Biyu Kishiyoyin Juna a Ivory Coast


Shugaba Allassane Outara da Laurent Gbagbo

Mutane biyu dinnan da kowannensu ke ikirarin cin zaben Shugaban Kasar Ivory Coast sun kafa gwamnatoci kishiyoyin juna jiya Lahadi.

Mutane biyu dinnan da kowannensu ke ikirarin cin zaben Shugaban Kasar Ivory Coast sun kafa gwamnatoci kishiyoyin juna jiya Lahadi.

Laurent Gbagbo, wanda ikirarinsa na zama wanda ya yi nasara a zaben ke samin goyon bayan Majalisar Kudin Tsarin Mulkin Ivory Coast, ya nada masanin tattalin arziki Gilbert Marie N’gbo Ake a matsayin sabon Firayim Minista. Shi kuma Alassane Outara, wanda Hukumar Zaben Ivory Coast ta ayyana a matsayin wanda ya ci zaben fid da gwanin na ran 18 ga watan Nuwamba, ya ce Firayim Minista na yanzu Guillaume Soro shi ne zai shuganaci gwamnatin tasa.

Mr. Gbagbo da Mr. Outara sun yi rantsuwar kama aiki a matsayin Shugaban ranar Asabar.

Tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Thabo Mbeki ya gana jiya Lahadi da Mr. Gbagbo da Mr. Outara.

Mr. Mbeki, wanda Kungiyar Hadin Kan Afirka ta tura shi Ivory Coast din don ya sasanta bangarorin biyu, yace yana kan tattaunawa da kowa don fahimtar al’amarin.

Mr. Outara ya fadi jiya Lahadi cewa ya gana da Mr. Mbeki ne a matsayinsa na halaltaccen Shugaban Ivory Coast. Ya ce ya shawarci tsohon shugaban na Afirka ta Kudu cewa ya shawo kan Mr. Gbagbo ya mika ragamar mulki.

XS
SM
MD
LG