Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta Goyi Bayan Ouattara


Mr.Alassane Ouattara wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ce shi ya ci zabe.

Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa Ouattara gaskiya a zaben kasar Ivory Coast.

Kwamitin Sulhun MDD ya goyi bayan shugaban ‘yan hamayya Alassane Ouattara a zama shi ne wanda yayi nasara a zaben shugaban kasar Cote D’Ivoire da aka yi a cikin watan jiya.

A cikin wata sanarwar da aka bayar da yammacin jiya laraba bayan shawarwarin kwanaki biyar, kwamitin mai kasashe 15 a cikin shi ya bukaci duka bangarorin da su mutunta sakamakon zaben ranar 28 ga watan Nuwamba.

Haka kuma kwamitin ya yi tur da Allah waddai da duk wani kokarin neman yin zagon kasa ga abun da jama’a ke so ko neman kassara ingancin matakin zabe ko kuma lalata zaben da aka yi a kasar Cote D’Ivoire cikin gaskiya da adalci.

Manzon MDD a kasar Cote D’Ivoire, Choi Young-ji, wanda aka dorawa nauyin sake nazartar sakamakon zaben, ya fada cewa Mr.Ouattara ya yi nasara da ratar da ba tantama, ta yadda shugaba mai ci Laurent Gbagbo ba shi da wata hujjar yin gardama.

XS
SM
MD
LG