Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka na Bayan Japan Dari Bisa Dari inji Trump.


Trump Tare Da Firaministan Japan Shinzo Abe
Trump Tare Da Firaministan Japan Shinzo Abe

Firayim minista Shinzo Abe na Japan da shugaba Donald Trump na Amurka sun mayar da martani su na yin tur da gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi

Firaministan kasar Japan Shinzo Abe yace makami mai linzami mai cin dogon zango da Koriya ta Arewa ta harba a tekun Japan “wani abune da sam ba za a yarda da shi ba."

Abe yayi bayanin ne a jiya Asabar tare da Shugaban Amurka Donald Trump a wani taron manema yada labarai na gaggawa da a kayi a dakin taro dake Katafaren Gidan Trump a Jihar Florida mai suna Mar-a- Lago inda Abe ya kai wa Trump ziyara a karshen Makon nan.

Jagoran gwamnatin na kasar Japan yace “Dolene Koriya ta Arewa tayi aiki da dukkan kudurorin Kwamitin Sulhun Mjalisar Dinkin Duniya,” kuma ya kara da cewa . “ A yayin tattaunawar da nayi da Shugaba Trump, ya tabbatar min da cewa Amurka zata kasan ce tare da Japan Dari bisa dari, domin nuna jajircewar sa akan al’amarin gashi tare da ni a wannan tattaunawa da manema labarai.”

A wajen tattaunawar da manema yada labarai Trump yayi kalamu da lafazi mai zafi yana cewa “Ina so kowa ya sani, ya kuma fahimci cewar Amurka na goyon bayan Japan, Babbar kawarta dari bisa dari,” Gwajin na Koriya ta Arewa anai masa kallon tsokana ne ga Gwamnatin Trump.

Koriya ta Arewa ta Harba Makamin mai linzami ne a Kogin Japan a safiyar lahadi Bangaren Asiya.

XS
SM
MD
LG