Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Kalubalanci Hukuncin Kotun Daukaka Kara


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai kalubalanci hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke, kan watsi da bukatar da ya gabatar mata na maido da umurnin nan da ya ya bayar na hana wasu ‘yan kasashe bakwai shiga Amurka.

A kwanakinsa na farko da karbar mulki Trump ya haramtawa kasashen bakwai da Musulmi suka fi rinjaye shiga Amurka saboda dalilai da ya ce na tsaro ne.

Kasashen sun hada da Iran da Iraq da Somaliya da Syria da Sudan da Libya da kuma Yamal.

Amma wata kotu a shiyya ta tara a jihar Washington ta dakatar da umurnin, matakin da shugaba Trump ya kalubalanta a kotun daukaka kara dake San Francisco.

Sai dai haka ba ta cimma ruwa ba, domin alkalan kotun su uku duk sun yi watsi da karar da Trump ya daukaka a gabansu a farkon makon nan, matakin da Trump din ya ce zai kalubalanta.

“Mun tsinci kanmu a wani yanayi, inda tsaron kasarmu ke cikin hadari, kuma wannan lamari ne mai matukar muhimmanci, saboda haka muna shirin gamuwa da su a kotu, sai mun yi nasara a wannan shari’a.” In ji Trump.

Bayan yanke wannan hukunci, Babban mai shari'a na jihar Washington, Bob Ferguson, wanda ya yi adawa da dokar ta shugaba Trump, ya ce wannan hukuncin nasara ce ga kundin tsarin mulkin Amurka.” Ferguson ya ce.

XS
SM
MD
LG