Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Jaddada Rashin Amincewa Da Hannun Yarima A Kisan Kashoggi


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Donald Trump ya bayyanar da matakin Amurka akan binciken kisan dan jarida Jamal Kashoggi.

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, “zai zama baban kuskure” a juya wa Saudiyya baya, duk da cewa akwai hannunta a kisan dan jarida Jamal Khashoggi da ke zama a Amurka.

Kafin ya kama hanyarsa ta zuwa hutun cika-ciki wanda ake kira ‘Thanksgiving’ a turance, Shugaba Trump ya fadawa manema labarai a fadar gwanati ta White House cewa, batun tsaron kasa da tattalin arziki ya fi duk wani batu na hakkin dan adam.

Trump ya kara da cewa Amurka na tare da Saudiyya, lura da cewa tana adawa da Iran, sannan tana wa Amurkan cinikin makamai na biliyoyin daloli, wanda hakan ke samar da ayyukan yi.

Trump ya ce “ba za mu ba Rasha da China sararin cin wata moriya ba” yana mai jaddada cewa farashin mai a kasuwar duniya zai tashi, idan har kawancen Amurka da Saudiya ya samu rauni.

Sai dai shugabannin kwamitin harkokin wajen Amurka a majalsiar Dattawan kasar, Bob Corker, na jam’iyyar Republican da Bob Menendez na Democrat, sun aikawa da Trump wata wasika, inda suka yi mai tuni cewa, dokar Amurka ta bukaci ya yi bincike ko Yarima Salman ne ya ba da umurnin kisan Khashoggi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG