Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Shirin Sakawa Iran Sabbin Takunkumi


Amurka ta ce ta shirya tsaf don sake kakaba sabbin takunkuman karya tattalin arziki ga Iran a yau Litinin, a kokarin da take yi na ganin gwamantin Iran ta sauya halayenta.

Amurka na shirin sake kakaba sabbin takunkumai akan Iran a yau Litinin, a wani yunkuri na kara durkusar da karfin tattalin arzikin kasar, da nufin sauya halayen gwamnatin ta Iran.

Sakataran Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya kira sabbin matakan a matsayin masu “muhimmanci” amma ya ki ya yi cikakken bayyani ga manema labarai kan wannan mataki da Amurkan ke shirin dauka gabanin a ayyana shi a hukumance.

Pompeo ya yi wadannan kalamai ne gabanin ya kama hanyarsa ta zuwa Saudi Arabiya da kuma kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, a wani yunkuri da gwamnatin Trump ke yi na tattaro kan kawayenta domin a kalubalanci Iran.

Ita dai Amurka tana kalubalantar Iran ne kan shirinta na mallakar makamin nukiliya.

Amma Iran din ta musanta cewa tana ci gaba da kera makaman, inda har ta kulla wata yarjejeniya a shekarar 2015 da Amurka, Birtaniya, China, Faransa, Rasha da kuma Jamus na takaita shirinta na mallakar makamashi, da nufin kawar da fargabar da ake nunawa, inda za a sassauta mata takunkuman da aka saka mata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG