Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Tare Da Najeriya Wajen Shawo Kan Kalubalen Tsaro: Jakada Mary Beth


Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard (ta biyu daga dama,) da ma'aikatan VOA, Medina Dauda (farko daga dama) Benjamin Gowon, (na biyu daga hagu) da Timothy Obiezu, wakilin sashen Ingilishi na VOA, yayin wata zantawa ta musamman da suka yi a Abuja

Jakadar kasar Amurka Mary Beth Leonard ta ce kasar Amurka na tare da Najeriya a wannan lokaci na kalubalen tsaro kuma zata bada gudumawa wajen ganin an shawo kan matsalar ta fanoni daban daban.

Jakadar ta yi wannan bayani ne a wata hira ta musamman da ta yi da Sashin Hausa a babban birnin taraiyyan Najeriya Abuja.

Jakada Mary Beth Leonard ta ce ko wane bangaren mulki da kuma jama'ar kasa na da rawar da za su taka wajen magance matsalar sha'anin tsaro da ta addabi sassa daban daban da kasar a wanan lokaci.

Mary Beth ta yi misali da irin barazanar data kunno kai a kasar Amurka a wattanin da suka gabata inda ta yi nuni da cewa hadin kan jama'a da fahimtar juna ta sa aka ci karfin al'amarin da take fata Najeriya da yan Najeriya za su yi koyi da shi.

Mary Beth Leonard ta ce ko da yake doka ta bada sararin mika koke ga gwamnati, amma kone kone da kashe kashe da suka auku a wani sashe na kasar babban laifi ne a bisa tsarin doka.

Mary Beth ta ce akwai hadari wajen gogawa wata al'umma kashin kaji, wato zargin aikata wani laifi na musamman a maimakon kama mai laifi a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Madam Leonard ta ce kasar Amurka za ta cigaba da taimaka wa Najeriya kamar yadda ta saba ta hanyoyi daban daban har da hanyar bunkasa noman abinci inda ta kai ziyara jihar Kebbi har ta halarci wani taro wajen yaye dalibai da aka horar a fanin noma.

Karin bayani akan: Amurka, Mary Beth Leonard, jihar Kebbi, Nigeria, da Najeriya.

Mary Beth ta ce kasar Amurka na kashe sama da dalar Amurka biliyan daya da rabi kowace shekara a matsayin bada tallafi.

Jakada Mary Beth Leonard ta yi na'am da kokarin da Najeriya ke yi wajen sasanta kasa da kasa domin wanzar da zaman lafiya musamman a kasashen Afrika inda ta yi misali da nada sabon Jakada da zai yi aiki a kasashen Mali da Chadi.

Leonard ta ta ce wannan ya jaddada shugabancin Najeriya a Nahiyar Afrika baki daya.

A karshe Mary Beth Leonard ta yaba da yadda 'yan Najeriya suke kar6an ta hannu bibbiyu ayawancin jihihin da ta kai ziyarar aiki irin su jihar lagos da Akwa Ibom da jihar Kebbi, da Plateau da kuma Sokoto a cikin shekaru biyu da ta yi tana aiki a kasar, inda ta ce ba don bullar cutar Korona Bairus ba, da yanzu ta karade dukanin Jihohin Kasar domin ta sa ido a yadda ayyukan tallafin da Amurka ke bayar wa suke gudana, sannan ta gana da mutane masu al'adu daban daban saboda ta kara sanin abubuwa a game da Najeriya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG