Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Fitar Da Sahaidar Dake Tabbatar Da Iran Ta Kai Hari Kan Teku


Donald Trump

Ma’aikatar Tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar da wasu sababbin hotuna wadanda ta ce sun dada tabbatar da cewa kasar Iran ce ta kai wa tankokin mai hari a tekun Oman a makon da ya gabata.

Amurka ta ce, daya daga cikin hotunan ya nuna wasu dakarun kasar Iran dauke da wani bangare da bai fashe ba na jikin tankar jirgin mallakin Japan, dayan hoton kuma ya nuna inda aka makala jikin tankar.

Wani hoton ya nuna babban rami a jikin banagren tankar.

Wasu daga cikin hotunan manema labarai da aka dauka a ranar Alhamis na nuna lokacin da tankin jirgin Norway, ke ci da wuta yayin da ya turnike da hayaki.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG