Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiya Ta Karu A Cikin Masu Zargin Iran Da Kaiwa Tankokin Mai Hari


Yarimar Saudi Arabia Mohammed bin Salman
Yarimar Saudi Arabia Mohammed bin Salman

Yarima mai jiran gado a Saudi Arabia ya zargi kasar Iran da kai hare hare a kan jiragen dakon mai a kan tekun Oman kana ya yi kira ga kasashen duniya su dau kwakkwarar mataki a kan wannan batu.

Abubuwar fashewa da suka lalata jiragen Norway wanda kamfanin Front Altair ke mallaka da kuma na kamfanin kasar Japan Kokuka Courageous ya faru ne a ranar Alhamis yayin da Firai ministan Japan Shinzo Abe yake wata ziyara a Tehran domin shiga tsakani a kan karin tankiya tsakanin Amurka da Iran.

Wata jaridar gwamnatin Saudi Arabia, ta rawaito kalaman yarima Mohammed Bin Salman, a wata hira da ya yi da manema labarai yana fadin cewa, Iran bata mutunta ziyarar da Firai ministan Japan ke yi a kasarta ba, ta mayara masa da martani da kai hare hare a kan jirage biyu ciki har da na kasarsa Japan.

Iran da ta musunta wannan zargin tana da hannu a wadannan hare hare, ta baiwa jakadar Birtaniya a Tehran sammaci a jiya Asabar bayan Birtaniya ta yiwa kasar zargin kai hare haren, a cewar kamfanin dillancin labaran Iran na ISNA.

A wannan zaman tare da jami’an ma’aikatar harkokin waje, Iran ta caccaki Birtaniya da kakkausar lafazi kuma tace ba zata lamunta da matsayar Birtaniya a kan batun hare haren tekun Oman.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG