Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gano Wasu Mambobin Kungiyar Hizbullah


Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken

Duk da cewa AQAH tana ikirarin yi wa mutanen Lebanon hidima, gaskiyar maganar ita ce suna aika kudade ta haramtacciyar hanya zuwa asusun ajiya, inda suke saka cibiyoyin kudaden Lebanon cikin hadari a saka masu takunkumi.

A ranar 11 ga watan Mayu, Ofishin Baitul Malin na Ofishin Kula da Kadarorin Kasashen Waje, ko OFAC, ya gano wasu mutane bakwai da ake dangantawa da Hizbullah da wani kamfanin hada-hadar kudi, Al-Qard al-Hassan, ko AQAH.

"Daga sama zuwa kasa na fannin hadahadar kudaden Hizbullah na ci gaba da tabka almubazzaranci da kudaden kasar Lebanon yayin da Lebanon ke cikin mummunan yanayi," in ji Daraktan OFAC Andrea Gacki. "Irin waɗannan ayyuka, suna nuna rashin damuwar Hezbollah game da, adana kuɗi, nuna gaskiya, ko bayar hukunci a Lebanon."

Duk da cewa AQAH tana ikirarin yi wa mutanen Lebanon hidima, gaskiyar maganar ita ce suna aika kudade ta haramtacciyar hanya zuwa asusun ajiya, inda suke saka cibiyoyin kudaden Lebanon cikin hadari a saka masu takunkumi.

AQAH na buya a bayan kungiya mai zaman kanta, yayin da take aiki a matsayin banki da ke tallafawa Hezbollah. Ta hanyar boye kuɗaɗe waɗanda tattalin arziƙin Lebanon ke buƙata, AQAH na taimaka wa Hizbullah ta gina hanyoyin samun kudadenta tare da nuna halin ko oho ga kasar ta Lebanon.

Shida daga cikin mutanen da OFAC ta gano, kan yi amfani da asusun ajiyar wasu bankuna na Labanon, gami da Bankin Jammal Trust da Amurka ta ayana, don kaucewa takunkumin da aka sa wa AQAH tare da tura kimanin dala miliyan 500 a madadin AQAH.

OFAC ta kuma sanya Ibrahim Ali Daher wanda ke aiki a matsayin Shugaban Babban Bankin Hizbullah. Wannan rukunin yana kula da kasafin kudi da kashewa na kungiyar Hizbullah, gami da samar da kudaden kungiyar ga bangarori na ayyukan ta’adanci, tsoratarwa, da kashe masu adawa da kungiyar.

Fito da mutanen da aka yi, na kara nuni da matakan da Amurka ke dauka na yaki da kungiyar ta Hizbollah. Amurka za ta ci gaba da daukan matakan da za su rika wargaza ayyukun kungiyar ta Hizbullah.

XS
SM
MD
LG