Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi Kasar Iran


Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Iran kashedi da kakkausar murya, yana mai barazanar fatattakarta idan ta kaiwa Amurka ko kuma kawayen Amurka hari.

Trump ya fada a wani sakonsa na Twitter a jiya Lahadi, yana cewa idan Iran tana so tayi fada, toh karshenta ya kai a hukumance. Yace kada ki kara nunawa Amurka hannu a cikin ido.

Wuni uku kacal kafin jiya, Trump ya bayyana alamun janyewa daga matsayinsa a baya na abkawa Iran, inda yake cewa zai koma kan teburin tattaunawa da Tehran.

A lokacin da wani dan jarida ya masa tambaya a fadar White House, ko Amurka zata yi yaki da Iran sai yace baya jin za a yi haka.

Amma kuma ga dukkan alamu tsugune bata kare ba tsaknin Amurka da kawayenta da kuma Iran a gefe guda.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG