Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Kara Shiri A Kan Daukar Matakan Soji A Kan Iran


Jiragen ruwan yakin Amurka

Amurka ta umarci ma’aikatanta da masu aikin gaggawa ba su fice daga Iraq, yayin da ‘yan majalisar dokokin Amurka suke bayyana fargaban shiga yaki da Iran.

Za a janye jami’an dake aiki a ofisoshin jakadancin Amurka dake Bagadaza da kuma Irbil ne a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Trump ta bayyana barazanar da dakarun Amurka a Gabas ta tsakiya suke fuskanta daga Iran da kuma sojojin hayar Iran.

‘Yan majalisa sun kushewa daukar wannan matakin da kakkausar murya a zauren majalisa.

Akwai dalilai biyu rak da zasu sa a umurci ficewar su: na farko nuna kwakkwaran bayanin leken asiri cewa mutanenmu suna cikin hadari, ko kuma ana shirin daukar matakin soji a kan Iran, inji babban dan jam’iyar Democrat a kwamitin hulda da kasashen ketare a majalisa Robert Menendex daga jihar New Jersey. Ya kara da cewa, Gwamnatin Trump bata gabatar da wadannan bayanan gaban kwamitin nan ba, da ya shafi rahotannin sirri da suka sa aka dauki wannan matakin ko kuma abinda suke shirin yi a Iraq ko Iran.

Menendez ya bukaci jami’an gwamnati su yiwa kwamitin cikakken bayani kan duk wani shirin shiga yaki da Iran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG