Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi Kasar Pakistan


A jiya Asabar Amurka ta gargadi kasar Pakistan da cewa idan har bata kama tare da hukunta malamin nan da ake zargi da kitsa harin 2008 da aka kai birnin Mumbai na Indiya ba, to tabbas dangantakar kasashen biyu zata sami matsala

Wannan gargadi dai ya biyo baya ne, bayan da jami’an Pakisatan ranar Juma’a su kayi amfani da izinin da kotu ta basu na cewa su saki Mallam Hafiz Saeed, mutumin da Amurka ta ayyana a matsayin ‘dan ta’adda, daga ‘daurin talala akayi masa domin rashin ingantacciyar shaida.

Tun shekarar 2012 Amurka ke tayin tukwicin dala miliyan 10 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka yi sanadiyar kama Saeed da hukunta shi.

Jiya Asabar fadar White House ta yi Allah wa dai da sakin Saeed da aka yi, tana mai cewa hakan aikawa da sakon da bai kamata bane, akan rawar da Pakistan ke takawa wajen yaki da ta’addanci a duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG