Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta kai harin makami mai linzami kan Libya


Harin makamai mai linzami kan LIbya.

Amurka da wadansu kasashen Turai sun kai hari kan kasar Libya

Amurka ta kai harin makami mai linzami kan mayakan saman kasar Libya, ta shiga sahun abokan kawancenta a yunkurin murkushe dakarun shugaban kasar Libya Moammar Gahdafi. Wani jami’in ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana jiya asabar cewa, jiragen ruwan Amurka da kuma na Birtaniya sun harba sama da makami mai linzami 112 samfarin Tomahawk kan wuraren da gwamnatin kasar Libya ke da iko jiya asabar. An kai hari kan sama da wurare 20 da suke barazana ga dakarun hadin guiwa da kuma farin kayan kasar Libya. Shugaban kasar Libya Moammar Gahdafi ya ci alwashin kare kasarshi daga abinda ya kira harin da bashi da adalci. Ya kuma ce zai bude rumbum ajiyar makaman kasar domin mutanen Libya su kare kansu. Mr. Ghadafi ya kuma lashi takobin maida martani kan sansanan soji da kuma farin kaya, bisa ga cewarshi harin da kasashen yammacin suka kai a Baharum ya maida wurin bakin daga. An ji karar harin sararin sama dukan dare a Tripoli. A halin da ake ciki kuma, dubban mutane sun taru a gidan da Mr. Gadfi yake zaune a birnin Tripoli wanda yake da cikakken tsaro, domin shinge shi daga duk wani harin da za a iya kaiwa gidan ta sararin sama.

Shugaban Amurka Barack Obama dake ziyarar a kasar Brazil yace , kasashen yammaci basu da wani zabi, illa daukar matakin soja kan Mr. Gahdafi. PM kasar Birtaniya David Cameron ya bayyana a birnin London cewa, matakin da aka dauka kan Mr. Gadhafi ya zama dole kuma ya yi daidai. Tun farko jiragen yakin kasar sun kai hari kan motocin yakin kasar Libya, harin kasar waje na farko da aka kai, na aiwatar da dokar tsaron sararin sama da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana kan Libya. Kakakin rundunar sojin kasar Faransa yace an kai harin ne kan wata motar sojoji dake barazana ga farin kaya a Libya, sai dai rahotanni na nuni da cewa, harin ya kuma lalata wadansu manyan tankunan yaki hudu dake dab da birnin Bengazi inda yan tawaye suke da karfi.

XS
SM
MD
LG