Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Libya ta Tsagaita Wuta Cikin Matsin Lambar Matakin MDD na Tsaron Sararin Samaniya


Ministan Harakokin wajen kasar Libiya a birnin Tarabulus Moussa Koussa ya na sanarwar Tsagaita wuta a Jumma'ar nan.

Gwamnatin kasar Libiya ta ayyana tsagaita wuta a fafatawar da ta ke yi da 'yan tawaye.

A yau Jumma'a gwamnatin kasar Libiya ta ayyana tsagaita wuta a fafatawar da ta ke yi da 'yan tawaye, da alamu wani mataki ne na amsa kudirin da Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya zartar kasa da kwana daya yanzu, wanda ya bada izinin yin amfani da dukkanin matakan da su ka wajabta don kare Fararen Hula a kasar ta yankin arewacin Afirka, a ciki kuwa har da sararin tsaron samaniyar da kasashen Majalisar Dinkin Duniyar su ka kwakubawa Libiyar.

Wani mutum na kallon taswirar shamakin tsaron sararin samaniyar da za a karfafa a kasar Libiya.
Wani mutum na kallon taswirar shamakin tsaron sararin samaniyar da za a karfafa a kasar Libiya.

A birnin Tarabulus ministan harakokin wajen kasar Libiya Moussa Koussa ya yi sanarwar tsagaita wutar. Ya ce gwamnatin shi ta na so ta fara tattaunawa da dukkannin masu sha'awar samar da hadin kan kasar Libiya. Da yake magana game da cewa nan kusa za a iya fara luguden wuta kan garkuwar tsaron samaniyar kasar Libiya, ministan ya karfafawa manyan kasashen duniya guiwar cewa su duba gaskiyar al'amuran da ke faruwa a kasar ta hanyar tura tawagogin jami'an gano gaskiya da sanin tabbas tukuna kafin su dauki wani mataki na kai tsaye akan gwamnatin shugaban kasar Libiya Moammar Ghadafi.

Koussa ya soki lamirin matakin da Kwamitin Sulhun ya dauka na bayar da izinin yiwuwar yin amfani da karfin soji, ya bayyana shi a zama wani abu "Bambarakwai kuma na rashin hankali da rashin tunani".Ya ce karfafa shata shamakin tsaro a sararin samaniya zai kara jefa al'ummar kasar Libiya cikin wahala.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar Libiya sun ce babban dalilin da ya sa su fita kan tituna a watan jiya domin yin tur da Allah da waddai da Mr.Ghadafi, shi ne nuna gajiya da wahalar tattalin arzikin da su ke fama da ita.

Wasu 'yan kasar Libiya masu zanga-zanga rike da tuta a kan wani tankin yaki a garin Benghazi.
Wasu 'yan kasar Libiya masu zanga-zanga rike da tuta a kan wani tankin yaki a garin Benghazi.

Libiya ta rufe sararin samaniyar ta da jijjifin Jumma'ar nan, daga majiyoyin diflomasiya su ka ce za a iya fara kai hare-haren jiragen sama a kowane lokaci.

Jim kadan bayan kuri'ar da Kwamitin Sulhun ya yi da yammacin jiya alhamis, kakakin gwamnatin kasar Faransa Francois Baroin da ministan tsaron kasar Norway Grete Faremo sun ce kasashen su za su shiga cikin gungun kasashen da za su dauki matakin soji akan Libiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kudirin ne da nufin hana sojojin gwamnatin Libiya ci gaba da aiki da munmunan matakin su na ba sani ba sabo don murkushe boren da Fararen Hula ke yi.

A daidai lokacin da jakadun kungiyar kawancen tsaro ta NATO ke tattauna hanyoyin karfafa kudirin na Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya a yau Jumma'a, sojojin da ke biyayya ga Ghadafi sun yi ruwan wuta a garin Misrata wanda ke hannun 'yan tawaye a yammacin kasar.

Kasashe goma ne su ka jefa kuri'ar amincewa da kudirin a yammacin jiya, babu kasar da ta sa kuri'ar kin amincewa. Kasashe biyar kuwa da su ka hada da Brazil da China da Jamus da Indiya da kuma Rasha sun ki kada kuri'a.

XS
SM
MD
LG