Amurka a jiya Juma’a ta yi watsi da batun soijojin Syria sun kwace ikon birnin Manbij dake arewa maso gabashin Syria, inda ake bata kashi tsakanin mayakan Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka da sojojin Turkiya, bisa bukatar Kurdawan Syria.
A cikin wata sanarwa, ma’aikatar sojin Syria tace dakarunta sun kwace muhimman wurare kuma ta kara da tabbatarwa al’ummar yankin cewa akwai cikakken tsaro ga ‘yan Syria da ma wasu dake zaune wurin.
Sai dai rundunar hadin gwiwa a jagorancin Amurka dake yaki da kungiyar IS a wurin ta maida martani ta sakon Twitter tana fadar cewa babu alamar gaskiya a wannan maganar.
Kana rundunar hadin gwiwar ta kara da yin kira ga duk wani mahaluki da ya mutunta ‘yancin Manbij da kuma tsaron mutaneta.
Facebook Forum