Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kushe Matakin Rasha A Ukraine


Jakadara Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley
Jakadara Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley

Sabuwar jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta kushewa matakin sojin da Rasha ke dauka a gabashin Ukraine Jiya alhamis, ta ce takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar zai ci gaba da aiki.

Nikki Haley ta fada yayin zamanta na farko a kwamitin sulhu tunda aka tabbatar da ita a matsayin wadda shugaba Donald Trump ya zaba ta wakilci Amurka a Majalisar Dinkin Duniya cewa, ‘Muna son inganta dangantakarmu da Rasha, amma abinda ke faruwa a gabashin Ukraine, wani abu ne da ake bukata a fita karara ayi allah wadai da matakin da Rasha ta dauka”.

Haley ta ce ba za a janye takunkumin da Amurka ta kakabawa Rasha ba, sai Rasha ta maida ikon yankin Crimea da ta mamaye ga Kyiv.

Tun farko jiya alhamis, sakataren baitulmalin Amurka ya sanar da sassauta wadansu ka’idoji da suka shafi harkar kasuwanci da hukumar tsaron Rasha FSB, duk da takunkumin harkokin sadarwar internet da tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya sanyawa Rashar .

XS
SM
MD
LG