Janar Michael Flynn mai ritaya ya yi Allah wadai da gwajin makamin inda ya bayyana shi a matsayin “ lokuta da dama da Iran ke yiwa Amurka da kawayenta barazana cikin watanni shida da suka wuce.
Ya ce Shuwagabannin Tehran sun bugi kirji da daukan matakin ne saboda “Yarjejeniyar tana da rauni kuma ba ta da amfani” kuma saboda kasashen da suke cikin wannnan yarjejeniyar sun ki daukan mataki akan burin dakarun kasar Iran.
A yayin da yake gabatar da takaitaccen jawabi a Fadar White house, Flynn ya soki tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama da sauran mambobin gwamnatinsa sun ki su dauki mataki kan irin karfin soji da hukumomin Theran ke nunawa.
Flynn ya kara da cewa “ Daga yau za mu saka wa Iran Ido .” ba tare da ya fayyace abin da ya ke nufi Amurkan za ta yi da Tehran ba.