Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Nemi a Warware Rikicin Ingilishi Da Faransanci a Kamaru


 Michael Hoza
Michael Hoza

Jakadan kasar Amurka, dake kasar Kamaru, Michael Steve Hoza, ya ziyarci shugaban Paul Biya, domin yi masa ta’aziya a fadarsa dake babban birnin kasar Yaoundé, kasancewar kasar ta yi rashi na manyan dakarun tsaronta hudu ciki harda mai kula da dakarun dake yaki da Boko Haram.

Jakadan na Amurka, ya ce ya je fadar shugaban ne domin mika ta’aziyar Amurka ga shugaban kamar yadda aka umarce shi da ya yi.

Ya kuma kara da cewa Amurka, na jinjinawa dakarun na Kamaru, akan irin rawar ganin da suke takawa wajan yaki da ‘yan Boko Haram, da kuma neman hanyoyin ci gaba da karfafa dankon zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.

Akan batun ‘yan awaren kasar ta Kamaru, kuwa jakada Hoza, ya ce Amurka na fatan za a warware rikicin cikin ruwan sanyi, yana kuma mai cewa dole ne a kyautata ‘yancin bil adama.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:51 0:00

XS
SM
MD
LG