Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Samu Wani Dan Najeriya Da Laifin Damfarar Miliyoyin Dala


Court hammer
Court hammer

Wata kotun tarayya da ke West Virginia a Amurka ta samu wani dan Najeriya mai suna Ayodele Arasokun da laifin damfarar gwamnatin Amurka dala miliyan 60 ta hanyar shigar da bayanan haraji na karya.

An sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da babban lauyan arewacin gundumar West Virginia ya fidda ranar Juma'a.

Sanarwar ta ce masu taimaka wa alkali yanke hukunci sun samu Arasokun da laifuffuka 21 da suka hada da zamba ta yanar gizo da kuma yin amfani da bayanan wasu yayin da ya kitsa shigar da takardun haraji na bogi guda 1,701 ya kuma nemi a maida masa dala miliyan 9.1.

'Yan yankin West Virginia na daga cikin wadanda aka sace bayanansu aka yi amfani dasu a damfarar, a cewar sanarwar.

Arasokun na a wani wuri da ke wajen birnin Paris na kasar Faransa a lokacin da aka aikata laifuffukan, amma sanarwar bata bayyana lokacin da suka faru ba.

Ma’aikatar Harajin Amurka (IRS) ta biya jimlar dala miliyan 2.2 na zamba, a cewar sanarwar.

jury-convicts-leader-worldwide-tax-return-scheme

Masu bincike sun gano cewa Arasokun ya bi diddigin asusun banki kusan 700 na mazauna Amurka da ke da sama da dalar Amurka miliyan 50, kuma a yayin shari’ar, shaidu sun nuna cewa ya sa hukumar IRS tura kudi a katinan cire kudi na banki ko asusun bankunan da ya ke sa musu ido.

XS
SM
MD
LG