Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Amince da Bukatar Amurka na Mika Mata DCP Abba Kyari


Atoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami, hagu, Abba Kyari, dama (Facebook/Instagram/Malami/Kyari)

Attoni Janar na Tarayya kuma ministan Shari'a Abubakar Malami  ya mikawa Shugabar babbar kotun Tarayya takardar bukatar neman mikawa Amurkan DCP Abba Kyarin don fuskantar shari'a dangane da batun taka rawa a damfarar da ake zargin Hushpuppy da aikatawa.

Abubakar Malami yace Najeriya ta dau wannan mataki ne biyo bayan bukatar da jami'an diflomasiyyar Amurka dake ofishin jakadancinta a Abuja suka mikawa Najeriya.

Najeriya inji Attoni Janar din ta amince da mika Abba Kyarin ne biyo bayan gamsuwa da cewa, batun bai da alaka da wani banbancin launin fata, addini, kasa ko ra'ayi, amma dai batu ne tsantsa dake da alaka da shari'a.

A hirar shi da Muyar Amurka, lauya da ke da kwarewa a tsarin mulki, Barrister Yakubu Sale Bawa ya bayyana cewa, ba haka kawai za a kai Abba Kyarin a mika shi ga Amurkan ba, sai kotun ta ga dacewar yin hakan.

Dangane kuma da batun da shari'ar da yake fuskanta a nan Najeriya kan batun safarar hodar Iblis, lauyan yace tunda batun shari'ar Amurkan ne ya fara kunno kai to yanzu ita za a fara, amma kuma za a iya ci gaba da batun shari'ar miyagun kwayoyinma a lokaci guda.

Masu fafutika a Najeriya irinsu Comrade Kabir Dakata na maraba lale da matakin gwnamnatin. Yana mai cewa magana ce ta shari'a. In yana da gaskiya, zai fidda kansa, in kuma yana da laifi, a mai hukunci.

Yanzu dai kallo ya koma babbar kotun Tarayya don ganin irin hukuncin da zata yanke akan wannan batu mai tsananin daurin kai da kuma ya dauki hankalin al'ummar Najeriya da ma wadansu kasashen duniya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG