Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abba Kyari: An Dakatar Da Wasu Manyan ‘Yan Sanda Daga Aiki Bisa Zargin Hannu A Safarar Hodar Ibilis


'Yan sandan Najeriya (Mun yi amfani da wannan hoto don yin misali ne) AP

Tuni kuma hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan ta aikewa da sufeto janar na ‘yan sanda wannan mataki da hukumar ta dauka

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan Najeriya ta dakatar da karin wasu manyan ‘yan sanda daga aiki biyo bayan zargin tafka aika-aika na taimakawa a badakalar safarar hodar iblis zuwa cikin Najeriya da ake wa mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba kyari.

Manyan jami'an dai su ne mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Sunday Ubua da mataimakin supritandan na ‘yan sanda James Bawa.

Dakatarwar ta fara aiki ne tun daga ranar Litinin 14 ga watan Fabrairun na wannan shekara.

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan kazalika ta kuma umarci Sufeta Janar da ya dakatar da wasu jami'ansa biyu masu mukamin sufeta da suma ake zargi cikin wannan badakala

Wata sanarwa da kakakin hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda Mr. Ikechukwu Ani ya sanyawa hanu ta ce manyan jami'an da aka dakatar din na aikine a sashen rundunar aiki da cikawa da DCP Abba Kyari ya jagoranta wato IRT, kafin dakatar da shi biyo bayan wani zargin na daban na damfarar Hushpuppy.

Dakatattun jami'an ‘yan sandan ana zarginsu da taka rawa wajen badakalar karbar hodar iblis da yakai DCP Abba kyari komar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wao NDLEA.

Tuni kuma hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan ta aikewa da sufeto janar na ‘yan sanda wannan mataki da hukumar ta dauka tun a jiya a wata wasikar da kwamishina na daya na hukumar wanda har ila yau Alkalin kotun koli mai ritaya ne mai shari'a Clara Ogunbiyi.

Wasikar mai take ''Bincike Kan Kwace Hodar Iblis Da Kuma Mikata Ga Hukumar NDLEA Da Ofishin DCP Abba Kyari Ya iI'' a cikinta an ce an dakatar da manyan ‘yan sandan ne bisa la'akari da tanaje-tanajen aikin gwamnati mai lamba 030406 har sai an kammala binciken zarge-zargen da ake masu.

XS
SM
MD
LG