Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Soke Wata Tsohuwar Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran


Mike Pompeo
Mike Pompeo

Amurka ta amsa umarnin babbar kotun MDD na cewa ta dage wasu takunkumi da ta kakabawa kasar Iran, ta hanyar yaga wata tsohuwar yarjejeniyar da ta kulla da Iran din tun shekarar alif 955.

“Iran ta kwashi lokaci mai tsawo tana watsi da yarjejeniyar,” a cewar sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ‘kara da cewa kamata yayi a ce ita ma Amurka ta fice daga yarjejeniyar tun shekaru masu yawa da suka wuce.

Iran ta kai ‘karan Amurka gaban babbar kotun MDD, tana mai cewa takunkumin da Amurka ta kakaba mata ya sabawa yarjejeniyar da suka kulla tun alif 955.

Amurka da tsohuwar kawartata ta kusa Iran, sun amince da yarjejeniyar ne, a wani bangare na dakile tasirin tsohuwar tarayyar Soviet a gabas ta tsakiya lokacin ake zaman dar-dar tsakanin Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet din.

A jiya Laraba ne dai ita kotun ta MDD ta yanke hukuncin hana Amurka anfani da takunkumin da ta saka wa Iran wajen hana a shiga da kayan agaji, magungunna, abinci da kayan aiki zuwa cikin kasar ta Iran, musamman masu alaka da tabattarda lafiyar masu tafiye-tafiye a jiragen sama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG