Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tallafawa Yan Gudun Hijirar Venezuela Dake Brazil


Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya isa kasar Brazil ranar Juma’a, inda ya ziyarci cibiyar tantance ‘yan gudun hijirar kasar Venezuela, yayin da ya yi kira ga dimokaradiya da kuma shugaban kasa Nicolas Maduro ya sauka daga kan Mulki.

Akwai yan gudun hijirar Venezuela kusan 250,000 da yanzu haka ke Brazil, yayin da kuma wasu 600 ke zuwa a kullum kafin a rufe iyaka saboda annobar coronavirus.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Araujo, Pompeo ya ce “Yan gudun hijira suna son dukkan abin da dan Adam yake so, mutunci, suna son dimokaradiyya da zaman lafiya da kuma kiran Venezuela gida, inda su da iyalansu da ‘ya ‘yansu su sami aiki da kuma rayuwa cikin mutunci. Mu Amurkawa da Brazil muna goyon bayansu.”

Ya kara da cewa yayin da babu wanda ya san lokacin da Maduro zai sauka daga Mulki, “Ranar na nan zuwa.”

Pompeo ya sanar da cewa Amurka za ta bayar da dala miliyan $348 domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Venezuela, ciki har da dala miliyan $30 ga ‘yan Venezuela dake kasar Brazil.

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG