Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Mayar Da Martani Ga Ziyarar Babban Jami’in Amurka Zuwa Taiwan


Kasar China ta aika da jiragen yaki kusan 20 zuwa sararin saman kasar Taiwan a wani nunin karfin soji da ba a saba gani ba, a wani martani ga ziyarar babban jami’in Amurka zuwa yankin tsibirin.

Jiragen sojojin China 18 ciki har da samfurin H-6 mai luguden bama bamai da kananan jiragen yaki, sun tsallaka iyakar Taiwan da safiyar Juma’a, a cewar sanarwar da ma’aikatar tsaron Taiwan ta fitar.

Keith Krach, mai kula da harkokin tattalin arziki na Amurka ya isa kasar Taiwan ranar Alhamis domin halartar taron tunawa da tsohon shugaban kasar Lee Teng-hui. Shine babban jami’i daga ma’aikatar harkokin wajen Amurka da ya ziyarci Taiwan a tsawon shekaru masu yawa.

China dai ta yi Allah wadai da ziyarar, “China za ta dauki matakin da ya dace daidai da abin da ya faru,” a cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ranar Alhamis.

Haka kuma, China ta aika da jiragen soji zuwa tsallaken iyakar Taiwan lokacin da sakataren ma’aikatar Lafiya ta Amurka, Alex Azar ya kai ziyara a watan da ya gabata.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG