Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Da Ke Fada a Afghanistan Sun Zargi Juna Da Kaddamar Da Sabbin Hare Hare


Bangarorin da ke fada a Afghanistan sun zargi juna da kaddamar da sabbin hare-hare a kasar, yayin da wakilansu suka yi ganawar tarihi a rana ta biyu a jiya Lahadi a birnin Qatar, ganawar samar da zaman lafiya da Amurka ta shiga tsakani. 

Fadan da aka yi tsakanin jami'an tsaron Afghanistan da mayakan Taliban a cikin sa'oi 24 da suka gabata ya yi sanadiyyar kisan mutane da dama a cewar rahotanni, ciki har da mayaka daga bangarorin biyu da kuma farar hula.

Har yanzu tashin hankalin da ake yi na zaman kalubale ga tattaunawar da aka dade ana jira wadda ake yi yanzu a Doha babban birnin Qatar, wadda ta hada da manyan wakilan da ke shawarwari daga bangaren ‘yan Taliban da gwamnatin Kabul.

Jami'an Amurka sun ce tattaunawar da ake yi tsakanin bangarorin biyu da ke fada a Afghanistan za ta maida hankali ne kan cimma "cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita" da kuma kulla yarjejeniya a siyasance da nufin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 40 ana yi a kasar da ke kudancin nahiyar Asiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG