Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Taya Najeriya Murnar Cika Shekaru 57 Da Samun ‘Yancin Kai


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Najeriya na bikin cika shekaru 57 da samun 'yancin gashin kanta daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya a daidai lokacin da Amurka ke jaddada shirinta na tallafawa kasar wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Sakatare harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya jaddada kudurin kasar na taya Najeriya yaki da kungiyar Boko Haram da kuma rassan kungiyar ISIS da ke yankin yammacin Afirka.

Tillerson ya kuma bayyana shirin Amurkan na tallafawa gwamnatin Najeriyar agazawa miliyoyin mutanen da rikicin na Boko Haram ya shafa domin su koma rayuwarsu ta da, tare da samar da makoma ta gari ga daukacin kasar.

Sakataren harkokin wajen Amurka, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, wacce Muryar Amurka ta samu, kan taya Najeriya murnar cika shekaru 57 da samun ‘yancin gashin kai, yayin da kasar ke bikin a yau daya ga watan Oktoba.

“Muna taya al’umar Najeriya murnar cika shekaru 57 da samun ‘yancin gashin kai.” Sanarwar ta bayyana.

Tillerson ya kara da cewa dangatakar Amurka da Najeriya, an gina ta ne akan muhimman tubalan da suka shafi tsaro da tattalin arziki da mulki na gari da kuma zimmar samar da kyakkyawar makoma.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG