Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Sanya Wa Shugabanin Houthi Takunkumi 


Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka
Antony Blinken, Sakataren Harakokin Wajen Amurka

Amurka ta ayyana wasu shugabannin mayakan Houthi guda biyu wadanda ke da alaka da ayyukan da ke ci gaba da haifar da rikici a Yemen, wanda ke zama babbar barazana ga fararen hula, da kuma kara munin bala’in jinkai a can.

Yakin Yemen ya fara ne a shekarar 2014 lokacin da ‘yan Houthi da ke samun goyon bayan Iran suka kwace babban birnin kasar, Sana’a daga gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita suka kuma kori shugaban Yemen din zuwa gudun hijira. Fadan da ya biyo baya ya haifar da daya daga cikin mafi munin bala’in jinkai a duniya, kuma kasar ta sake fadawa kan barazanar yunwa. Akalla mutane miliyan 20 sun dogara da wasu nau'ikan taimakon jinkai don rayuwa.

Shugabannin biyu da Amurka ta ayyana a ranar 20 ga watan Mayu, dukkansu suna da hannu a yakin Houthi kan yankin Marib da ke karkashin ikon gwamnati. A kwanan nan Muhammad Abd Al-Karim al-Ghamari ya dauki nauyin kai harin; Yusuf al-Madani, wanda a da ya kasance kwamanda a wasu larduna daban-daban a Yemen, yanzu an sanya shi a cikin yakin da ake kaiwa Marib.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa da ke bayyana sunayen, Sakataren Harkokin Wajen Antony Blinken ya ce, "Wannan harin na Marib yana kara dagula rikicin jinkai na Yemen, yayin da ya sanya kimanin mutane miliyan daya da suka rasa muhallinsu cikin hatsarin sake yin gudun hijirar, kuma alumun barazanar zai fi karfin ayyukan agaji.

Ayyukansu na nufin cewa, an toshe damar amfani da duk wata dukiya da kaddarori da ke cikin Amurka na wadanda aka sa wa takunkumi, an kuma haramta wa Amurkawa duk wata ma'amala da waɗanda suka haɗa da irin waɗannan mutane ko kadarorin.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Blinken ya lura cewa ayyukan Houthi suna da mummunan tasiri a kan fararen hula kuma hakan na faruwa ne “duk da cewa ba a taba samun yarjejeniya a tsakanin kasashen duniya da masu ruwa da tsaki a yankin kan bukatar tsagaita wuta nan take da kuma sake komawa tattaunawar zaman lafiya ba.”

Ya ce, “Muna kira ga Houthi da su hanzarta dakatar da duk wasu hare-hare da kuma kai hare-hare na sojoji, musamman farmakin da suke kaiwa kan Marib, wanda hakan ke kara haifar da wahala ga mutanen Yemen. Muna rokon su da su guji ayyukan dagula lamura su shiga kokarin Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman don samar da zaman lafiya. "

Sakatare Blinken ya kara da cewa, "Lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan rikici."

XS
SM
MD
LG