Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Kashedi Na Hari A Kan Jirgin Dakon Man Saudiya


Jirgin Ruwa

Kasar Saudi Arabia tace tankokinta biyu sun yi mumunar lalacewa a wani harin ganganci da aka kai da safiyar shekaranjiya Lahadi a gabar tekun Hadaddiyar Daular Larabawa. Sai dai ba a bada wani karin bayani a kan lalacewar ba.

Ministan makamashi a Saudi Arabia yace daya daga cikin jiragen dakon man yana kan hanyar shi ne zuwa tashar jiragen ruwan Saudiya ta Ras Tanura domin daukar mai ta kai Amurka.

Amurka ta fitar da wata takardar kashedi da safiyar jiya Litinin game da zargin harin gangancin a kan jiragen ruwa dake gabar tekun Hadaddiyar Daular Larabawa, haka zalika a makon da ya gabata Amurka tayi kashedi ga jiragen ruwan Iran da na wakilanta, da ka iya auna jiragen ruwa a yankin. Kashedin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun tankiya tsakanin Amurka da Iran.

Jami’ai a ma’aikatar tsaron Amurka sun fadawa Muryar Amurka cewa, sojojin Amurka suna taimakawa wurin gudanar da bincike a kan harin barna da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawan ta bukaci a gudanar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG