Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Watsi Da Ikirarin Rasha Akan Mallakar Makaman Gama Duniya


Sakataren Tsaron Amurka Janar James Mattis
Sakataren Tsaron Amurka Janar James Mattis

Ikirarin Rasha na cewa ta mallaki makaman nukiliya da ka iya kai koina a duniya ba tare da ganinsu ba ya sa Amurka ta yi watsi da ikirarin kuma ta na ganin wata alama ce daban da ba zata razana Amurka ba

Amurka ta yi watsi da ikirarin da shugaban kasar Rasha Vladimir Puttin yayi na cewa kasarsa na da jerin sabbin makaman nukiliyar da zasu iya kaiwa ko ina a cikin duniya.

Fadar White House ta shugaban Amurka da kuma ma'aikatar tsaro sun yi watsi da wannan ikirari a zaman wani babatu kawai, suna masu cewa ba suyi mamaki da jin cewa Rasha tana sabunta makamanta na nukiliya ba, haka kuma wannan ba zai razana Amurka ba.

Mai magana da yawun fadar White House, Sarah Sanders, ta ce, "Shugaba Putin ya tabbatar da abinda Amurka ta jima da sani ne. Ta ce Rasha ta shafe shekaru fiye da 10 tana kirkiro makamai masu gurgunta zaman lafiya, abinda ya keta alkawuran da ta dauka karkashin yarjejeniyoyi da dama.

Ta kara da cewa Amurka tana ci gaba da kokarin sabunta makaman nukiliyarta tare da tabbatar da cewa babu wata kasa a duniya da zata iya kamo kafarta a fagen soja, inda ta yi misali da sabon kasafin kudin tsaro na Dala miliyan Dubu 700 da aka gabatar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG