Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Binciken Rasha: Wata Hadimar Trump Ta Fuskanci Tambayoyin 'Yan majalisa


Hope Hicks yayin da ta kammala amsa tambayoyi
Hope Hicks yayin da ta kammala amsa tambayoyi

A ci gaba da binciken zargin katsalandan din da Rasha ta yi a zaben Amurka na 2016, wata jami'a a gwamnatin shugaba Donald Trump, ta amsa tambayoyin kwamitin majalisar dokokin Amurka.

Shugabar ofishin yada labaran Shugaban Amurka Donald Trump Hope Hicks, wacce ta kasance cikin dadaddun hadiman da suka yi wa Trump aiki, ta bayyana gaban kwamitin majalisar dokokin Amurka.

Hicks ta bayyana ne don amsa tambayoyi akan alakar wadanda suka yi wa Trump yakin neman zabe da Rasha.

Sai dai ba ta amsa tambayoyin da ‘yan majalisar suka yi mata ba akan watanni 13 da ta yi tana aiki a Fadar shugaban kasa ta White House.

Kwamitin binciken bayanan sirri ya yi wata ganawa da Hicks ta tsawon sa’o’i da dama.

Hicks ta yi wa iyalin Trump aiki a matsayin mai magana da yawun 'yar shugaban Amurka Ivanka Trump, a bangaren tallata tufafin da take sayar wa kafin daga baya ta shiga yi wa Trump yakin neman zabe a lokacin da ya tsaya takarar da ya sami nasara a shekarar 2016.

Dan majalisar wakilai, Adam Shiff, jigo a jam’iyyar Democrat da ke kwamitin, ya fadi cewa Hicks ta amsa tambayoyi game da yakin neman zaben Trump, da lokacin zaben zuwa lokacin da aka rantsar da Trump a matsayin shugaban kasa.

Amma ba ta ce komai akan lokacin da ta yi aiki a Fadar shugaban kasa ta White House ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG