Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Zargin Mataimakin Shugaban Sudan Ta Kuda Da Cin Zarafin Bil Adama


Shugaban Sudan ta Kudu President Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu President Salva Kiir

Gwamnatin Amurka ta sanya takunkumi akan mataimakin shugaban Sudan ta Kudu na farko Taban Deng Gai, tana mai zargin sa da aikata manyan laifukan keta hakkokin bil Adama da kokarin kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya a kasar da yaki ya daidaita.

A wata sanarwa da aka fitar jiya Laraba, ofishin dake sa ido kan kadarorin kasashen duniya a Amurka da ake kira OFAC a takaice, ya ce Deng, ya yi kokarin haifar da rarrabuwar kawuna da haddasa shakku a tsakanin ‘yan jam’iyyar SPLM-IO ta kasar, jam’iyyar dake adawa da shugaba Salva Kiir.

Sanarwar ta kara da cewa, matakan da ya dauka sun tsawaita rikicin da ake yi a Sudan ta Kudu, sun kuma gurgunta kokarin yin sulhu da samar da zaman lafiya bayan yakin basasar da aka kwashe shekaru biyar ana yi.

Haka kuma sanarwar ta ce, rahotanni sun bayyana cewa Deng, ya kitsa tare da ba da umarnin kisan wani lauyan kare hakkokin bil Adama mai suna Samuel Dong Luak da kuma Aggrey Idry dan jam’iyyar SLPM-IO, a kokarin karfafa matsayinsa a gwamnatin Kiir don kuma tsorata mambobin jam’iyyar ta SLPM-OI.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG