Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Wani Tsohon Hadimin Pompeo Ya Yi Allah Wadai Da Shisshigin 'Yan Siyasa


Wani babban hadimin Sakataren harkokin wajen Amurkan Mike Pompeo, ya fadawa masu binciken da ke duba yiwuwar tsige Shugaba Trump cewa, ya ajiye aikinsa ne a makon da ya gabata saboda yadda ake saka siyasa a ma’aikatar harkokin wajen kasar, inda har ya yi nuni da yadda Shugaba Trump ya sallami tsohuwar jakadiyar Amurka a Ukraine Marie Yovanovitch.

A tsawon sa’o’in da ya kwashe yana amsa tambayoyi a gaban kwamitin, Michael McKinley, ya yi Allah wadai da yadda ma’aikatar ba ta kare hakkin jami’an diflomasiyanta irinsu, Marie daga shisshigin‘yan siyasa.

Wannan bahasi da McKinley ya bayar a gaban kwamitin tattara bayanan sirri na majalisar wakilai, wanda tuni da ma wasu jami’a da ke da masaniyar abubuwan da ke faruwa suka bayyana, shi ne labari mara dadi na baya-bayan nan da aka gabatar a gaban kwamitin, kan yadda ake kumbiya-kumbiya wajen gudanar da ayyukan harkokin wajen Amurka da na hukumomin tsaronta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG