Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: 'Yansanda Sun Tsare Mutane 20 Daren Litinin a Ferguson


'Yansandan Ferguson yayin da suke kama masu zanga-zanga

‘Yan sanda sun tsare sama da mutane 20 dake zanga-zanga daren jiya Litinin a garin Ferguson dake Jihar Missouri a nan Amurka, lamarin da har yanzu yake jawo zaman tankiya shekara daya da aukuwar harbin wani matashi Micheal Brown mai shekaru 18.

Wannan matashi bashi da makami a lokacin da wani dan sanda farin fata ya harbe shi. Jami’ai sun ayyana dokar ta baci, amma hakan bai hana cigaba da samun arangamomi ba tsakanin masu gangami da ‘yan sanda a dare na biyu da ake cigaba da ganin tashe-tashen hankula a unguwar dake kusa da birin St. Louis.

Yayin da gari ka yin duhu ne, masu zanga-zanga da yawa suka yi watsi da umarnin da ‘yan sanda suka basu, na cewa kar su toshe tituna, musamman titin West Florissant Avanue, inda aka samu tashe-tashen hankula a shekarar da ta gabata.

Saboda matsalolin da yanzu ake fuskanta musamman ganin ana wannan bukin cika shekara daya da kashe Brown, akwai wasu jama’a masu zanga-zangar dake ganin cewa lamarin ya kara budewa jama’a idanu.

Wani mazaunin garin Ferguson mai suna Mal Stiff yace ana zargin jama’a da wuce-gona-da iri, amma kisan Micheal Brown abu ne da ake ta kokarin boyewa. Yace abun ya kayatar da shi, saboda akwai darrusan koya.

Wata mace kuwa mai suna Tiffany Shawn cewa tayi abubuwa da yawa sun canza a zukatan jama’a, musammam masu zanga-zanga da kuma jama’ar da suke son gani an samu canji.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG