Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Ci Gaba Da Baiwa NATO Goyon Baya


Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence jiya Litini ya jaddada matukar goyon bayan da Amurka za ta ci gaba da nuna ma NATO da Turai.

Sai dai kuma ya ce har yanzu wasu kasashen Turai da dama ba su da abin da ya kira "cikakke kuma sahihin tafarki" na kara kason kudin da su ke ware ma bangaren tsaro balle ma har su biya kasonsu a karo-karon da ake a wannan kungiyar da ta kai shekaru 10 da kafuwa.

Da ya ke jawabi a hedikwatar NATO da ke Brussels, Pence ya bayyana cewa Amurka ce kawai da wasu kasashe hudu daga cikin jimlar kasashe 28 da ke cikin kawancen ke cika ka'ida ta ware kashi 2% tattalin arzikinsu kan tsaro.

"Mu na ma da niyyar kara yawan kudin da mu ke kashewa kan tsaro. Amurka za ta cigaba da sauke nauyin da ya rataya a wuyanta," a cewar Pence da ya ke bayyana aniyar sabuwar gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump. To amma sai ya kara da cewa, "Yanzu fa lokacin aikatawa ne, ba lokacin surutu kawai ba" da ya koma kan kasashe 23 da ba su cika ka'aidar ta akalla kashi 2%.

Pence ya samu goyon bayan Sakatare-Janar din NATO Jens Stoltenburg, wanda ya ce, "Ina mai cikakken goyon bayan raba nawaya. Abin farin ciki shi ne mun dau harma."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG