Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Dauki Mataki Kan Shige Da Ficen Baki


Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa za ta dauki wani kwakkwaran mataki akan harkar shige da ficen baki a yau Laraba.

Shugaba Trump wanda ya bayyana haka a shafinsa na Twitter da safiyar yau Laraba, bai yi cikkaken bayani akan matakan da zai dauka ba.

Duk da haka, Trump ya bayyana yadda dokokin kare iyakar Amurka suke da rauni matuka idan aka kwatanta su da na Mexico da Canada ba da suke da karfi sosai,

Shugaban ya yi wadannan kalaman ne kwana daya bayan ya fadawa manema labarai cewar zai tura sojoji zuwa kan iyakar Amurka da Mexico don dakile hanyoyin shige da ficen baki ba bisa ka’ida ba.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta maida martini akan wannan shiri na amfani da sojoji don gadin iyakar kasa, inda wani jami’inta ya ce suna nan suna tattaunawa da Fadar White House akan lamarin.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG