Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Da Dama Ne Ke Neman A Tsige Trump Kafin Wa'adinsa


Shugaba Trump

Kashi 57 cikin 100 na Amurkawa na so a sauke shugaba Donald Trump daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba, bayan da shugaban ya karfafa zanga-zangar da aka yi a wannan makon wadda ta rikide ta koma mummunar tarzoma a cikin ginin majalisar dokokin Amurka.

Hakan ya bayyana ne a cikin wani binciken jin ra’ayoyin jama’a na kamfanin dillancin labaran Reuters da IPSOS.

Yawancin mutanen da suke so a sauke shugaban ‘yan Democrat ne, ko da yake yan Republican da yawa na goyon bayan a bar shugaban ya kamala wa’adinsa, wanda zai kare ranar 20 ga watan Janairu.

Haka kuma binciken jin ra’ayoyin jama’a na kasa, wanda aka yi a ranakun Alhamis da Juma’a, sun nuna cewa mutun 7 cikin 10 da suka jefawa Trump kuri’a a zaben watan Nuwamba sun nuna rashin amincewarsu da matakin da masu goyon bayan shugaban suka dauka na afkawa ginin majalisar dokokin a yayin da ‘yan majalisar ke zaman tabbatar da nasarar da Joe Biden na jam’iyyar Democrat ya samu a zaben watan Nuwamba.

A gefe guda kuma, Wani dan majalisar jiha mai goyon bayan Trump wanda ya dauki bidiyon kansa ya na shiga ginin majalisar dokokin kasar da kuma wani mutun dan jihar Arkansas wanda ya dauki hoton kansa ya na zaune a ofishin shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi na daga cikin masu tarzoma sama da 10 da masu gabatar da kara na gwamnatin tarayya ke tuhuma a babban binciken da suke yi game da harin da aka kai ranar Larabar da ta gabata a ginin majalisar dokokin kasar, a cewar jami’an gwamnatin tarayya jiya Juma’a.

Ana tuhumar Derrick Evans, dan majalisar wakilai a jihar Virginia daga jam’iyyar Republican akan shiga wurarren da sai da izini ake shiga a ginin majalisar. Evans ya yada bidiyon kansa a shafin FB a lokacin da ya afka cikin ginin tare da wasu masu tarzoma, akwai lokacin da aka ji ya na cewa “mun shiga ciki.”

A wani bidiyon da ya sanya a FB kafin lokacin kuma wanda daga baya aka cire, Evans ya yi gargadin cewa masu tarzomar zasu shiga ginin majalisar.

XS
SM
MD
LG