Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Aika Sojojin Afirka Dubu 10 Don Fatattakar Sauran 'Yan Boko Haram


A wuraren da Boka Haram suka addaba a kasashen Nijar, Kamaru, Chadi da Najeriya, yanzu haka an kai musu sojojin Africa har dubu 10 domin su fatattaki sauran da suka rage a wadannan wuraren.

Boko Haran ce dai tayi dalilin mutuwar mutane har sama da dubu 20, tun daga lokacin da ta fara tada kayar baya a shekarar 2009 a jihohin arewa maso gabashin Najeriya.

Ayyukan ta’addancin su yasa mutane da yawan su ya kai sama da miliyan 2 rasa muhallansu a wadannan kasashen 4, Yanzu haka mutane sama da miliyan 20 na zaune cikin halin kila wa kala.

A shekarar 2015 sai da kungiyar tarayyar Africa ta umurci sojojin kungiyar ta hadin gwiwa da ta fatattaki tungar kungiyar ta Boko Haram dake arewa maso gabashin Najeriya da kuma arewacin Kamaru.

Yanzu haka dai rundunar tana kwace wuraren da kungiyar boko haram din ta kame sannu a hankali, domin ko an kwace wasu yankunan da boko haram ta kwace da niyyar kafa daular Islama a kasashen yammacin Africa.

Rundunar tayi nasarar fatattakar kungiyar zuwa cikin kungurmin daji daga sassan da ta ke da tasiri wani lokaci can baya.

Sai dai wannan nasarar da sojojin na kungiyar tarayyar Africa su ka samu, ya kawo ma da yawan fararen hula koma baya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG