Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bankado Wasu Bayanai A Kan Yakin Habasha Da Yankin Tigray


Rikicin Habasha
Rikicin Habasha

Wata mace da ta yanke shawarar ficewa daga gidanta bayan ta tsorata da harebe harben bindiga a kusa da gidanta a yankin Tigrya dake arewacin Habasha ta karu a cikin jerin mutane masu yawa da suka je ofishin karamar hukuma neman takardar barin kasar.

Amma yayin da ta isa ofishin, sai jami’an ofishin suka fada mata cewa ta bata lokaci.

Sun ce “wannan wuri ne na wadanda suka amince su yi yaki.”

Yayin da gwamnatin Habasha ta shiga yaki da yankin Tigray da kuma neman kama shugaban yanki da ya bijire, wanda yake kallon gwamnatin tarayya haramtacciya bayan ya ware kansa, wannan yaki da ka iya hargitsa yankin Kurya Afrika na boye da abubuwa da kasashen waje basu gani. Sadarwa ta lalace, ana rufe hanyoyi kana an rufe filayen saukar jiragen sama.

Amma a lokacin da aka dauke mutane daruruwa kalilan a wannan mako daga Tigray, wannan matar da Associated Press ta tattana da ita, ta bayyana wasu batutuwa da ba kasafai a ke jinsu ba na fushi da tashin hankali da kuma tsananin yunwa yayin da bangarorin biyu suka yi biris da kirar da kasashen duniya ke yi ga tattaunawa ko kuma kai kayayyakin jinkai a yankin, a daidai lokacin da yakin ya shiga mako na uku. Majalisar Dinkin Duniya ta ce abinci da abubuwan rayuwa zasu kare a yankin nan bada dadewa ba, lamarin da zai jefa miliyoyi mutane cikin hadari.

Ganin yanda ake hana shigar da kayayykin jinkai a Tigray kana ma’aikatan jinkai ‘yan kalilan ne ke amfani da wayyoyin taurarin dan Adam suna tuntubar duniya, yasa ba a samun cikakken bayani a kan mutane dake shan wahala a wurin. An kashe daruruwan mutane kana Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare haren dake auna farar hula saboda kabila ko addinin su.

Matar, ‘yar kasar Habasha kuma masaniya a kan aikin jinkai da ta nemi a boye sunanta saboda jin tsoron rayuwarta da na ‘yan uwanta, ta bada cikakken bayani a kan mutum miliyan shida da basu da abinci, ba fetur, ba kudi, ba ruwa ba wuta, yayin da sojojin gwamnatin Habasha ke kara dannowa kusa da babban birnin yankin Tigray.

Ta ce “Ina fada muku, sannu a hankali mutane zasu fara mutuwa.”

A lokacin da rufe iyakoki da hanyoyi da filayen saukar jiragen sama bayan firai ministan Habasha ya sanar cewa sojojin Tigray sun kaiwa tungar soji hari ne wannan mata ta shiga tashin hankali, saboda tana da ‘yan uwa a Addis Ababa kuma tana so ta je wurin su.

An rufe bankuna amma ‘yan uwanta sun bata isasshen kudi da zata iya zuwa Mekele. Yayin da take kan hanya, sai ta ratsa gefen shingaye da matasan yankin suka kafa da duwatsu. Sai dai ta ce bata ga yaki a kan hanyan ta ba.

A Mekele, ta ga abokan arziki a jami’ar wurin. Ta kuma ce kadu da abubuwa da ta gani.

XS
SM
MD
LG