Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Ya Barke Tsakanin Yankin Tigray Na Habasha Da Eritrea


Firai Ministaqn Habasha, Abiy Ahmed.

An kai wasu hare haren roka a jiya Asabar a babban birnin Eritrea, Asmara, a cewar ‘yan difomasiya, sa’o’i kalilan bayan da yankin Tgray na Habasha ya yi kashedin yiwuwar kai hari.

Rokokin sun auna filin saukar jiragen sama na babban birnin kasar. Sai dai babu wani labari game da adadin barna da mutuwa da ta faru, kana jami’an yankin Tigray basu ce komai ba.

A ranar Talata ne shugaban kungiyar ‘yan tawaye People's Liberation Front (TPLF), ta yankin Tigray, Debretsion Gebremichael, ya zargi Ertrea da aika runduna a kan iyakar kasar su taimakawa dakarun gwamnatin Habasha, zargin da ministan harkokin wajen Eritrea Osman Saleh Mohammed ya musunta a wata hira da ya yi da Reuters. Ya ce “ bamu cikin wannan yaki.”

Eritrea ta dade tana zaman doya da manja da kungiyar ‘yan tawayen TPLF, a cewar masana, kana tana jin tsoron za a saka ta a cikin yakin TPLF da gwamnatin tarayyar Habasha.

Da yammacin ranar Juma’a ne Tigray ta harba rokoki a filayen saukar jiragen sama guda biyu dake kusa da yankin Amhara, inji hukumomin Habasha da na yankin Tigray.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da hare haren, tana mai fada a cikin wata sanarwa cewa, an harba rokokin ne zuwa garuruwan Bahir Dar da Gondar. Sakamakon haka wani bangaren filin saukar jiragen saman ya lalace.

An kashe daruruwan mutane tun lokacin da firai minister Abiy Ahmed ya tura rundunar tsaron kasa zuwa Tigray a ranar 4 ga watan Nuwamba, bayan da aka zargi rundunar yankin da kai hari a kan tungar soji.

Sama da ’yan kasar Habasha dubu 14 sun arce zuwa kasar Sudan kana hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai wasu da dama kuma dake kan hanya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG