Accessibility links

An Bude Kasuwar Baje Kolin Kayan Masarufi A Kano

  • Grace Alheri Abdu

Wata mace a kasuwa
Cibiyar kula da harkokin ciniki, masana’antu, ma’adanai da ayyukan noma ta jihar Kano ta shirya kwarya-kwaryar baje kolin kayayyakin masarufi da nufin siyarwa jama’a a farashi mai rangwame saboda Azumin Ramadan.

Wadanda suka ziyarci kasuwar baje kolin sun bayyana cewa, ana samun kayan masarufi da rahusa, yayinda hukumomi suka bayyana daukar matakan sa ido domin ganin bata gari basu yi amfani da wannan dama wajen cutar talakawa ba.

Alhaji Mohammed Dahiru Yusuf mataimakin shugaban hulda da jama’a na ma’aikatar ya yiwa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari karin haske a kan shirin.

XS
SM
MD
LG