Accessibility links

Jama'ar Adamawa Zasu Fara Azumi Cikin Mawuyacin Hali


Muulmai lokacin bikin sallah

Jama'ar Adamawa zasu fara azumi cikin mawuyacin hali sabili da illar dokar ta baci ta jawo ma mutane.

Jihar Adamawa na daya daga cikin jihohi uku a arewa maso gabashin Najeriya da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kakabawa dokar ta baci.

Daka duk alamu jama'ar jihar zasu fara azumi cikin wani mawuyacin hali sanadiyar dokar ta baci da suke ciki. Sabili da takaita fita waje masu sayen abinci ko sayar da abinci lamarin ya katse masu kasuwa. Jama'a na tsoron kasancewa waje domin kada dokar hana fita ta kama su. Masu sana'ar yamma kaman masu sayar da kosai abun ya fi shafarsu. Lokacin azumi da yamma ake soya kosai da dama kunun da za'a sayar.

Dangane da samun wayar sadarwa yanzu sai mazaunan jihar sun tafi jihar Taraba kafin su samu su yi waya. Akwai wasu matsalolin da jama'a ke fama dasu sabili da dokar. Sai dai wasu kananan kuhumomi sun ce zasu taimakawa masu karamin karfi kamar masu sayar da shayi, tsire, yin toye-toye da dai sauransu.

Ganin yadda a kan samu tashin hankali a wannan lokacin limamai sun yi taron hadin kai domin su waye wa mutanensu kawuna don a zauna lafiya.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayan.

XS
SM
MD
LG