Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Taron Kolin Kasashen Afrika a Addis Ababa


Zauren taron kolin kasashen Afirka
Zauren taron kolin kasashen Afirka

An fara taron kolin na kungiyar kasashen Afirka a karo na 29 a birnin Addis Ababa, inda shugabannin kasashe suka hallara domin tattauna matsalolin da ke addabar kasashen nahiyar.

An bude taron kolin kungiyar hadin kan kasashen Afrika karo na 29 a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya ba da tallafin dala miliyan daya ga kungiyar.

Kimanin kashi 60 cikin 100 na kasafin kudin kungiyar yana fitowa ne daga tallafin kasashen ketare, da suka hada da Kungiyar tarayyar Turai, da Babban bankin duniya, da kuma kasashen da ba sa cikin kungiyar.

Mugabe ya dade yana bayyana bukatar ganin kungiyar ta dogaro da kanta.

Ya fada a wani jawabi da ya yi a tashar talabijin ta kasar Zimbabwe cewa,

“Afrika tana bukatar ta dauki nauyin ayyukanta”. Bai kamata kungiya kamar AU ta rika dogara akan tallafi ba, wannan ba abu ne da zai dore ba.

Kungiyar tana da kasasfin kudin dala miliyan 782 a shekarar a 2017 a watan Yulin bara, shugabannin kungiyar ta AU suka amince su sa tarar 0.2 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigowa da su nahiyar, domin samun kudin gudanar da ayyukan kungiyar.

A halin da ake ciki kuma. Shugaban kungiyar hadin kan Afrikan Moussa Faki Mahamat ya ce batun zaman lafiya da harkokin tsaro sune suke ci gaba da haifar da fargaba a nahiyar.

Taron kolin na kwanaki biyu, zai kuma maida hankali kan inganta rayuwar matasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG