Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Najeriya Ta Dakatar Da Yarjejeniyar Shell


kamfanin Shell
kamfanin Shell

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International da sauran kungiyoyin kare hakkin bil adama a ranar Litinin sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da yarjejeniyar da kamfanin Shell ya yi na sayar da wasu kadarorinsa a matsayin wata hanya ta tabbatar da hakkokin al’ummar yankin.

Al’ummomin da ke noma da kamun kifi a yankin Neja-Delta, cibiyar samar da danyen mai a Najeriya, sun shafe shekaru suna shari’a kan barnar da malalar mai yake yi a yankin.

Kamfanin Shell ya amince ya sayar da kadarorinsa da ke gabar tekun kasar ga wata kungiya mai cibiya a Najeriya kan kudi dala biliyan 2.4 yayin da ya koma harkokin kasuwanci a karkashin teku.

A wata wasika da aka fitar a ranar Litinin, Amnesty da sauran kungiyoyin kare hakkin Najeriya da na kasa da kasa sun yi kira ga hukumar da ke kula da harkokin Najeriya da ta ki amincewa da sayar da kadarorin Shell ga Renaissance African Energy.

Wasikar ta ce "Bai kamata a bar Shell ya yi waswasi da shari'a ba don guje wa alhakin da ya rataya a wuyansa na tsaftace gurbacewa da ya bari," in ji wasikar.

Ya kara da cewa, bai kamata a ba da izinin sayar da kadarorin Shell ba, sai dai idan har an tuntubi al’ummomin yankin, don a tantance gurbacewar muhalli da aka yi a halin yanzu, da kuma samar da kudaden da za a kashe wajen tsaftace muhalli.

Shell bai amsa bukatar yin sharhi nan take ba.

Kamfanonin mai sun ce suna gudanar da ayyukansu ne bisa tsarin mafi kyawun muhalli na fannin kuma suna zargin yawancin malalar da ake samu a kan zagon kasa da barayin mai da ke fasa bututun mai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG