Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wani Mutum Dauke Da Hodar Cocaine a Bakin Iyakar Najeriya Da Nijar


Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kaddamar da bincike akan wani mutum da aka kama da hodar cocaine da aka kiyasta kudinta ya kai naira biliyan daya.

Mutumin da aka kama mai suna Nkem Timothy dan asalin jihar Abia mazaunin kasar Algeria ya yi yunkurin tsallakawa da hodar ta cocaine ta bakin iyakar Najeriya da Nijar da ke garin Illela a jihar Sakkwato.

Komandan hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a Sakkwato Bamidele Segun Emos ya ce an tsayar da mutumin domin bincike sai aka tarar da daurin wasu abubuwa 62 da ake tsamani hodar cocaine ce a cikin jakar sa ya tsattsaga cikin robobin yogurt.

Komandan ya kara da cewa da aka matsa da karin bincike a cikin jakkar tasa an gano wani fasfo na shiga kasashen Ecowas wanda ke dauke da hoton sa amma sunan dake kan fasfon din ya bambanta da sunan da ya bayar da farko.

Sunan da ke kan fasfo din shine Awwalu Audu kuma fasfon da yake amfani da shi ke nan, tuni mun garzaya da shi a hedikwatar ofishin mu dake Sakkwato don ci gaba da bincike kuma yana ba mu hadin kai, muna son mu gano ko akwai wasu masu hannu ga wannan safarar" a cewar komandan.

Da aka tuntubi mai sharhi akan lamurran yau da kullum kuma masanin halayyar dan adam Farfesa Tukur Muhammad Baba ko me irin wannan ke nufi ga Najeriya? ya ce wannan ya nuna cewa wani bala’i kan bala’ o’i ne.

Shima Nura Andullahi Attajiri yana cikin masu fafatukar fadakarwa akan illolin sha da safarar miyagun kwayoyi ya ce duk irin wannan dabi’a na alaka da sauran matsalolin da ake fama da su yanzu.

Masu lura da al'amurra na ganin cewa muddin ba'a hukunta masu irin wannan laifin ba to ba za'a daina samun masu aikata wannan aikin ba.

Saurari rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00


An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG