Accessibility links

An Fara Ciyar da Marasa Lafiya Kyauta a Asibitocin Jihar Borno

  • Garba Suleiman

Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno yana ziyarar marasa lafiya a asibitin garin Baga.

Gwamna Kashim Shettima ya kafa wani kwamitin da zai kula da aikin ciyar da marasa lafiyar da har an fara gudanarwa a wasu asibitocin dake babban birnin jihar.

Gwamnatin Jiohar Borno ta fara rarraba abinci sau uku a kowace rana ga marasa lafiya, kyauta, a wasu asibitocin dake Maiduguri, babban birnin jihar, a wani sabon shirin da gwamna Kashim Shettima ya bullo da shi na ciyar da marasa lafiya kyauta a duk fadin jihar.

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu, wanda ya zaga asibitin Umaru Shehu a Maiduguri, yace gwamna Kashim Shettima ya kafa wani kwamitin da zai rika sanya idanu kan yadda za a rika dafa abinci ana ba marasa lafiyar, musamman wadanda suke kwance a kan gadajen asibiti, domin sawwake wa iyalansu wahalhalun da zasu yi ta fuskanta.

Wakilin na VOA, ya ganewa idanunsa yadda ake dafa abinci, wanda ma'aikatan dake aikin suka ce ya hada da kowane irin nau'i na abinci, ciki har da abinci na musamman da suke yi ma masu fama da ciwon sukari da masu hawan jini.

Marasa lafiyar da dama da suka tattauna da Haruna Dauda, sun bayyana jin dadi da gamsuwar wannan abu, kuma suka ce ana ba su abinci mai kyau, kuma da yawan da yake wadatar da su.

Har mutanen da suke zama su na jinyar marasa kafiya ma sun ce su na samun wannan abinci a asibitin na Umaru Shehu.

Wasu daga cikin masu aikin dafawa da rarraba abincin sun roki gwamna Kashim Shettima da ya kara musu kan Naira dubu 10 da ake biyansu, inda suka bayyana cewa su na kashe dunbu 6 daga cikin kudin wajen biyan kudin sufuri kawai zuwa bakin aiki.

XS
SM
MD
LG