Accessibility links

Kawo yanzu adadin wadanda aka akashe a Izige na karuwa bisa ga rahotannin ganau

Kawo yanzu adadin wadanda 'yan bindiga suka kashe a Izige jihar Borno dake makwaftaka da karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa sai karuwa yake yi.

Shaidun gani da ido sun ce adadin wadanda 'yan bindigan suka kashe sun fi mutane dari yayin da kuma wasu dubbai suka yi gudun hijira. Wani yace yaran da 'yan bindigan suka kawo cikin masallacin izala kana suka kashesu su arba'in da bakwai ne. Wadan da kuma aka kashe cikin kauyen sun kai dari. Bayan haka sun shiga gida gida suna kashe maza.

Daya daga cikin shugabannin karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa Mr. Maina Onarebul ya tabbatar da aika-aikar ya kuma ce fiye da mutane dubu goma ne yanzu ke gudun hijira domin haka ya bukaci masu bada agajin gaggawa su kai masu doki. Yace "sun fi dubu goma. Yanzu haka mutanen gari ne suke basu abinci. Babu abun da gwamnati ta yi. Mutane yanzu suna kwana gidin bishiya"

Kwamandan rundunar soja na ashirin da uku dake Yola Janaral Nicholas Rogers ya bayyana cewa tuni aka kara sojoji a yankin Madagali kodayake ya koka da rashin samun bayanai a kan kari.Yace "lalle an kara sojoji kan iyakan Madagali amma kuma babu yadda za'a ce sojoji na koina domin abubuwan nada yawa. Ina gani ma akwai matsalar samun bayanai daga al'ummomin yankin akan kari sai lokaci ya kure"

Ana fata Allah Ya kawo karshen zubar da jini a kasar.

XS
SM
MD
LG