Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Jana'izar Wadanda Suka Mutu a Wutar Dajin Girka


Wutar Dajin Da Ta Auku a Girka

Girka ta fara binne wadanda mummunar wutar daji ta kashe bayan da wutar ta afkawa wani yankin mai farin jini ga 'yan yawon bude ido da ke gabashin birnin Athens a makon jiya.

Jami'an 'yan kwan-kwana sun kara adadin wadanda gobarar dajin ta halaka zuwa 91, kuma akwai mutane 25 wadanda har yanzu ba'a san inda suke ba, bayan wutar ta ratsa ta yankin ranar Litinin ta makon jiya.

Daruruwan mutane ne suka halarci addu'o'i na musamman da aka yi a gari da ake kira Mati, wurin mafi farin jini ga 'yan yawon bude ido, inda gobarar ta fi barna.

Jami'an kwana-kwana suka ce galibin mutanen gobarar ce ta halaka su, wasu kuma ruwan teku ne ya halaka su yayin da suke kokarin tserewa daga wutar.

Hukumomin Girka sun ce da gangan aka ta da wutar, kuma ta yi saurin yaduwa ne sanadiyar yanayi na hunturu da ake fuskanta.

Bayanai sun nuna cewa wannan wutar daji ita ce mafi muni da aka gani a nahiyar turai tun bayan 1900.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG