Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zabe A Cambodia Ba Tare Da Babbar Jami'iyar Adawa BA


Frai Ministan Cambodia Hun Sen a Runfar Zabe
Frai Ministan Cambodia Hun Sen a Runfar Zabe

An bude zabe a Cambodia inda 'yan kasar zasu zabi wakilan majalisar kasa 125, a cikin wani tsarin zaben da ya sha sukar lamiri, sakamakon rashin masu adawa ga jami’iyar Cambodina People’s Party mai mulkin kasar.

Sa’ao’I kafin fara zaben, gwamnati ta bada umarni ga kamfanonin dake bada layukan internet da su rufe shafukar yanar gizon gidajen jaridu da na yada labarai 15, ciki har da Muryar Amurka da Radio Free Asia da kuma jaridar Phnom Penn Post

Phos Sovann shine babban jami’I mai kula da bayanai da watsa labarai a ma’aikatar yada labarai ta kasar, ya tabbatar da wannan labarin, kana Muryar Amurka ta samu wannan bayani a rubuce a wata takarda da ta samu daga ma’aikatar yada labaran.

Rusa babbar jami’iyar adawa ta Cambodian National Rescue Party da kotun kolin kasar ta yi a bara, yasa ana kyautata zaton firayi ministan kasar Hun Sen kuma dan takararr Cambodian People’s Party mai mulki ne zai lashe zaben.

Jami’iyar ta lashe zabuka a baya, wanda ke bata wa’adin shekaru biyar biyar. Shi kuma Hun Sen ya dere kan mulkin kasar kimanin shekaru 30.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG